June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mun gamsu da yadda jami’an soji suke gudanar da ayyuka a Katsina

1 min read

Gwamnatin jihar Katsina ta nuna gamsuwar ta bisa aikin da jami’an soji da sauran jami’an tsaro ke yi wajen dawo da zaman lafiya a jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai bai wa gwamnan jihar ta Kastina shawara kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina.
Sanarwar ta ce, shakka babu hadakar jami’an tsaro dake tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al’umma a jihar suna iya kokartinsu wajen ganin lamura sun kyautata.
Haka zalika sanarwar ta kara da cewa, akwai bukatar jami’an soji su ci gaba da yin rangadi a yankunan da rashin tsaro yayi kamari don dakile duk wani yunkuri na ‘yan ta’adda.
Sanarwar ta kuma godewa kafafen yada labarai wajen wayar da kan al’umma, game da matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *