June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zamu cigaba da daukar matakai a kasuwarmu-Sabon Gari

1 min read

Hukumomi a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da aka fi sani da kasuwar Sabongari a nan Kano, sun ce, za su yi iya kokarinsu wajen ganin cewa, ciki da wajen kasuwar sun kasance a ko da yaushe a yanayi mai tsafta.
Manajan darakta na kasuwar Alhaji Uba Zubairu Yakasai ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.
Alhaji Uba Zubairu Yakasai ya kuma bukaci ‘yan kasuwar da dukkan nin masu ziyartar kasuwar da su kasance suna sanya takunkumin rufe baki da hanci a duk lokacin da za su shiga kasuwar don kare kai daga cutar corona.
Manajan darakta na kasuwar ta Sabongari, ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su rika biyayya ga dokokin da aka sanya musu wajen rufe shagunansu da misalin karfe shida na yammaci, domin kuwa duk wanda aka kama shagonsa a bude bayan karfe shida za a hukuntashi.
Da ya ke gabatar da jawabi, daraktan mulki na kasuwar, Alhaji Muhammad Bashir Mai-Unguwa, kira yayi ga ‘yan kasuwar da su hada kai don bunkasa harkokin tattalin arziki a kasuwar da ma jihar Kano baki daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *