June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Abubuwan da suka faru a Najeriya makon da ya gabata

2 min read

A makon da ya gabata ne dai Gwamnan jihar Borno Babbagana
Umara Zulum ya zargi jami’an tsaron Najeriya da yin zagon ƙasa a
yunƙurin da ake yi na murƙushe ‘yan ƙungiyar Boko Haram.
Hakan ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wani hari da aka kai wa
Zulum ɗin a hanyarsa ta zuwa Baga.
Babagana Umara Zulum ya ce ba zai iya yin shiru cikin yanayi na
kashe-kashe ba, saboda rantsuwar da ya yi tsakaninsa da Allah a kan
zai kare al’ummar jiharsa.
Sai dai daga baya hedikwatar tsaro ta Najeriya ta fitar da sanarwa
inda ta musanta zargin da gwamnan Borno yake yi cewa sojoji ne
suka kai masa hari.
A cewar sojin, ‘yan Boko Haram ne suka kai hari, ba kamar yadda ake
cewa zagon kasa ne daga wajen jami’an tsaro ba. A makon da ya gabata ne Shugaban Najeriya Muhammadu, ya ba da
umarnin a sake fasalin baki ɗayan harkokin tsaron kasar domin
magance matsalolin da ake fuskanta.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana
Monguno ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala
taron majalisar tsaron ƙasar a Fadar Aso Rock.
A cewar Monguno, Shugaba Buhari ya buƙaci manyan hafsoshin
tsaron ƙasar su sake dabaru ta yadda za a shawo kan matsalolin
tsaro a yankin arewa maso yammaci da kuma arewa maso tsakiyar
Najeriyar.
Galibin ‘yan Najeriya da masu sharhi kan lamarin tsaro da kuma ‘yan
majalisun tarayya na da ra’ayin cewa ci gaba da zaman manyan
hafsoshin sojin a kan muƙamansu na daga cikin manyan abubuwan
da suke tarnaki ga yaki da ƙungiyar Boko Haram. A makon da ya gabata ne jami’an tsaron Najeriya suka tarwatsa
masu zanga-zangar Revolution Now a Abuja, babban birnin ƙasar.
Wani jigo a zanga-zangar ya ce an kama mutum aƙalla 60.
An kama wasu daga cikin masu zanga-zangar ne da safiyar Laraba a
Dandalin Unity Fountain kafin daga baya a sake kama wasu a
Shataletalen Berger da ke Utako.
‘Yan sanda ba su bayyana laifukansu ba zuwa yanzu.
Shugaba ko kuma wanda ya ƙaddamar da zanga-zangar, Omoyele
Sowore ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa jami’an tsaro sun ci
zarafin masu macin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *