June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Babbar matsalar da bangaren shari’a ke fuskanta shi ne rashin lada wanda suka cancanta-Osinbajo

1 min read

Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya caccaki wasu daga cikin ‘yan bokon kasar nan da masu fada aji wadanda ya ce, suna yin ruwa da tsaki wajen nada alakalai a kotunan kasar nan.

A cewar mataimakin shugaban kasar wannan matsala tana daya daga cikin dalilan da ke kara lalata bangaren shari’a.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wajen wani taro kan zaban alkalai wanda ya gudana a Lagos.
Ya ce, sdaboda haka ya sanya gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen ganin an tsaftace bangaren shari’a.

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce abin takaici ne yadda ‘yan boko da ‘yan siyasa har ma da bangaren masu zaman kansu ke sanya baki wajen tabbatar da cewa alkalan da za a nada sun dace da muradunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *