Bani da niyyar tsayawa takarar shugaban Kasa-Elrufa’i
1 min read
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce, ba ya da wani shiri na neman shugabancin kasar nan a shekarar 2023.
Mallam Nasiru Ahmed El-Rufai ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da tashar BBC.
Ya ce, ya kamata mulki ya koma kudancin kasar nan a shekarar 2023, bayan wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Malam Nasir El-Rufai ya ce ya sha ji ana yadawa cewa yana son shugabantar kasar nan tun yana minista na birnin tarayya, amma duk wannan zance ne kawai marar tushe
Ya kuma ce, a tsarin siyasar da ake yi a Najeriya, akwai tsarin da ake bi na karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan arewa ta yi mulki shekara takwas, kudu za ta yi mulki shekara takwas.
Ya ce duk da ba a rubuta tsarin karɓa-karɓar a tsarin mulki ba, amma kowane ɗan siyasa a ƙasar nan ya san da shi.