September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Boko Haram: Gwamnonin Arewa na so a bai wa ‘yan sanda makamai su tunkari kungiyar

1 min read

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya ta bukaci
gwamnatin tarayya ta kara azama a yaki da kungiyar Boko Haram a
yankin.
Gwamnonin sun yi kiran ne yayin taron kungiyar gwamnonin arewa
maso gabas da ya gudana ranar Asabar a Maiduguri, babban birnin
jihar Borno.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Borno Mallam Isah Gusau, ya
shaidawa BBC cewa a yayin taron, gwamnonin sun cimma matsaya
a kan batutuwa da dama, ciki har da bukatar gwamnatin shugaba
Muhammadu Buhari ta samar da karin makamai na zamani ga
sojojin da ke yaki da ayyukan ta’addanci a yankin.
Sannan sun bukaci a suma ‘yan sanda a samar musu makamai na
zamani domin taimakawa sojoji wajen yaki da kungiyar Boko Haram
da ta addabi yankin.
”Ko da yake gwamnonin sun yabawa kokarin gwamnatin Najeriya
game da matakan da take dauka ta fuskar yaki da ta’addanci, sai dai
sun ce akwai bukatar ta sake tashi tsaye domin kawo karshen
wannan matsala” in ji Isah Gusau.
Sun kuma zabi gwamnan Borno Babagana Umara Zulum, domin
zama shugaban kungiyar da zai jagorance ta har nan da shekaru biyu
masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *