September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya samar da kusan naira biliyan biyu a 2019

1 min read

Hukumar kula da sufurin jirgin ƙasa ta Najeriya wato Nigeria Railway
Corporation (NRC), ta bayyana a ranar Juma’a cewa ta samu kuɗin
shiga naira biliyan 3.09 a 2019 ta hanyar zirga-zirgar jiragen a faɗin
ƙasar.
Mista Fidet Okhiria wanda shi ne babban daraktan hukumar, ya
bayyana hakan a wata sanarwa a madadin minsitan sufuri, inda ya ce
sun samu naira biliyan 1.5 ne daga jirgin Abuja zuwa Kaduna.
Okhiria ya ce jirgin Abuja zuwa Kaduna yana samar da kusan naira
miliyan 130 duk wata a 2019, saɓanin miliyan 80 da aka riƙa samu a
2018.
Ya ƙara da cewa kuɗin da aka samu daga jirgin na Kaduna, an yi amfani
da su ne wurin gina sauran tashoshin jirgin ƙasa a yankin Arewa kamar
tashoshin Maiduguri.
“Jirgin hanyar Abuja-Kaduna ya samar da fiye da miliyan 130 duk wata,
yayin da muka kashe miliyan 90 wurin biyan albashin ma’aikata da
tafiyar da jirgin a tashoshin Maiduguri, waɗanda yanzu ba sa aiki
saboda matsalolin tsaro,” in ji shi.
Shugaban NRC ɗin ya ce a gefe guda kuma, ɓarkewar annobar korona
a Najeriya za ta shafi hasashen kuɗin da ya kamata a samu na
shekarar 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *