April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jonathan ya gargadi ‘yan siyasa kan tashin hankali

1 min read

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gargadi
‘Yan siyasar kasar da su kaucewa duk wani yunkurin da
zai haifar da tashin hankali, yayin da ya roke su da su
rungumi hanyar inganta zaman lafiya da cigaban kasa. Jonathan dake jawabi ga taron shugabannin Yan kabilar sa ta Ijaw
yace ya zama wajibi Yan siyasa su sanya cigaban kasa a gaba,
domin kuwa abinda siyasa ke bukata kenan amma ba raba kan
jama’a ko kuma yaki da abokan gaba ba.
Tsohon shugaban yace a matsayin sa na mai fafutukar ganin
dimokiradiya da shugabanci na gari ya wanzu a Najeriya da Afirka,
bukatar sa itace ganin jama’ar sa sun taka gagarumar rawa wajen
zabin wanda zai jagoran ce su da kuma yadda ake jagorancin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *