June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Masu garkuwa sunyi garkuwa da matar wani dan majalisa

1 min read

Masu garkuwa da mutane sun kama matar Dan majalissar jiha mai wakiltar karamar Hukumar Gwiwa a jihar Jigawa.

Masu Garkuwar su 6, sun shiga garin Tsubut dake karamar hukumar Gwiwa da misalin karfe 3 na daren ranar Juma’a, inda suka shiga gidan Dan majalisar Hon. Aminu Zakari Tsubut, suka kuma tafi da matar sa Malama Ruakayya.

Wasu Al’ummar garin sun ce masu Garkuwar sun nemi a basu kudi kafin su sako matar ta koma gidan mijinta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa CP Usman Sule Gwamna ya tabbatar da afkuwar lamarin, harma yace jami’an su na cigaba da aikin bincike don ceto matar daga hanun masu Garkuwar.

Haka kuma ya bukaci al’umma su rika yin gaggawar kai rahoton duk wani motsi da basu gamsu da shiba.
A cewar wani matashi karo na biyu da masu Garkuwar da mutane suka dauki matan ‘yan majalissa a jihar, inda koda a cikin watan yuni ma sun dauke matar Dan Majalissa jihar mai wakiltar karamar Hukumar Miga, kuma sai da aka biya kudi sannan suka sakota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *