July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Matasan Nigeria miliyan zasu samu guraren ayyukan yi- Osinbajo

1 min read

Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya kara jaddada matsayar gwamnatin tarayya na kirkiro da guraben ayyuka akalla miliyan biyar ga al’ummar kasar nan

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a a jiya, yayin wani taro da cibiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta jihar Lagos ta shirya wanda aka gudanar ta kafar Internet.

Ya ce, gwamnati tana kokarin bunkasa bangaren aikin noma da samar da gidaje masu rahusa da bunkasa masana’antu wanda hakan za su taimaka gaya wajen samar da ayyukan yi ga miliyoyin ‘yan Najeriya.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga masu sha’awar zuba jari daga ketare dana cikin gida don rage rashin ayyuka tsakanin matasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *