June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan sandan Katsina sun ‘kashe ‘yan fashi takwas’ tare da ƙwato shanu

1 min read

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce ta
kashe wasu da ‘yan fashi takwas sannan ta ƙwato shanu 30 a Ƙaramar
Hukumar Batsari da ke jihar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito kakakin
rundunar, SP Gambo Isah yana bayyana hakan ranar Asabar a birnin
Katsina.
Ya ce a ranar Alhamis 6 ga watan Agusta ne DPO na Batsari ya
jagoranci rundunar Operation Puff Adder zuwa ƙauyen Zamfarawa
sakamakon wasu bayanan sirri da suka samu cewa wasu ‘yan fashi
kusan 40 sun kai hari.
Ya ƙara da cewa ‘yan fashin sun kashe wani da ake kira Shafi’i
Suleiman mai shekara 65 da kuma Yakubu Idris ɗan shekara 70 tare da
yin awon gaba da shanu da dama.
A cewarsa, ‘yan fashin sun tare jami’ansu a kan hanyarsu ta zuwa
ƙauyen amma ‘yan sandan sun mayar musu da martani, inda suka
kashe ɗaya daga cikinsu.
Sai a ranar Juma’a kuma ‘yan sanda suka tsinci gawar mutum bakwai
da suka tsere da raunukan harbin bindiga a cikin daji, in ji SP Gambo.
“An samu kuɗi naira 22,300 a jikin mamatan da kuma tarin mukullaye
haɗi da layu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *