September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ambaliyar ruwa tayi sanadiyyar mutuwar 20.

1 min read

Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane Ashirin yayin da wasu sha uku suka jikkata a kasar Sudan a jiya Lahadi
Ambaliyar ruwan dai ita ce mafi muni da kasar ta fuskanta a baya bayan nan, sakamakon mamakon ruwan sama da kasar ke fuskanta a kowacce shekara tsakanin watannin Yuni zuwa Oktoba.
Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar rushewar jidaje dari uku da arba’in da biyar a fadin kasar, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 20 sai kuma mutane sha uku suka jikkata.
Wannan dai shi ya kawo adadin wadanda suka rasa rayukan su sanadiyyar ambaliyar ruwan ya kai 35, yayin da a kalla gidaje dubu bakwai suka ruguje tun daga farkon watan Yulin shekara da muke ciki.
A ranar Larabar da ta gabata ne majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa ambaliyar ruwa a bana za ta yi sanadiyyar rasa mahallai akalla mutane dubu Hamsin.
Hakane ya sanya rundunar tsaro ta Civil Defence ta aike da jirgin shalkwabta zuwa gabashin kasar inda ma’ikatan hakar ma’adanai ke aiki don kiyaye lafiyar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *