December 11, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Bude Makarantun Sakandare A Jihar Kano bisa wasu sharadai

2 min read

A yau litinin aka bude
makarantun sakandare a jihar Kano domin daliban da
ke ajin karshe, don shirye-shiryen tunkarar rubuta
jarabawar karshe da za’a fara kasa da makwanni biyu
masu zuwa, wadda hukumar shirya jarabawa ta Afrika
ta yamma wato WAEC da takwararta ta NECO ke
shiryawa a kowacce shekara.
Tun a makon jiya ne wasu daga cikin jihohin Najeriya
kamar jihohin Jigawa da Lagos suka bude nasu
makarantun, bayan cimma yarjejeniya akan haka
tsakanin hukumomin ilimi da babban kwamitin yaki da
cutar Coronavirus na kasar.
Jumlar dalibai 27,464 ne daga makarantun gwamnati
da na masu zaman kansu a jihar Kano za su rubuta
jarabawar kammala karatun sakandaren, sai dai
gwamnati ta hade cibiyoyin rubuta jarabawar mallakar
ta zuwa 33 maimakon 199, kamar yadda kwamishinan
ilimi na jihar Kano Alhaji Sanusi Sa’idu Kiru ya
shaidawa wakilin muryar Amurka.
Gabanin komawar daliban da ake sa ran zai wakana a
yau Litinin, tun Juma’ar da ta gabata ne gwamnati ta
kaddamar da aikin feshin kashe cuttuka da kwari a
ajujuwa da harabar makarantun domin tarbar daliban.
Kwamishinan muhalli na Kano Dr. Kabiru Ibrahim
Getso, ya ce aikin ya kunshi makarantun gwamnati da
na masu zaman kansu.
Baya ga feshi a makarantun, hukumomin jihar Kano
sun ce za su raba takunkumin rufe baki da hanci ga
daliban, tare kuma da samar da sinadarin wanke
hannu da kuma na’urar auna zafin jikin bil’adama a
dukkanin makarantun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *