Coronavirus a Najeriya: Mutum 437 sun kamu da cutar ranar Lahadi
2 min read
Hukumomi sun ba da rahoton gano sabbin masu cutar korona 437
ranar Lahadi, da wannan ƙari, yawan mutanen da annobar ta shafa a
Najeriya yanzu ya kai 46,577.
Alƙaluman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ke fitarwa
kullum, sun nuna cewa cutar ta kuma yi sanadin mutuwar mutum
uku cikin sa’a 24.
A Lagos, an sake gano mutum 107 da suka kamu ranar Lahadi, duk
da yake, ƙididdigar da ake fitarwa a baya-bayan nan na nuna alamun
lafawar cutar a can.
Haka zalika, bayanan hukumar NCDC sun bayyana cewa marasa
lafiya 142 sun warke daga cutar kuma an sallame su daga cibiyoyin
kwantar da masu korona na ƙasar.
Har yanzu akwai marasa lafiyan da ke ci gaba da jinyar cutar korona
12,446 a faɗin Najeriya, bayan warkewar kimanin mutum 10,000 a
ranar Talata. Wuraren da aka sake gano masu cutar da yawa, akwai Abuja babban
birnin Najeriya, inda mutum 91 suka kamu. A Filato, an ba da rahoton
cewa korona ta harbi mutum 81.
Sai Kaduna, inda aka gano sabbin masu cutar 32. A jihar Ogun,
mutum 30, ga kuma wasu 24 a jihar Kwara.
Mutum 19 kuma sun ɗauki cutar a jihar Ebonyi, sai Ekiti, an gano
marasa lafiya 17. Daga jihar Oyo, mutum takwas.
Jihohin Borno da Edo, mutum shida-shida ne aka samu da cutar
cikin kowaccensu. sai mutum huɗu a jihar Kano.
A Nasarawa da Taraba da Osun, mutum uku-uku aka ba da rahoton
kamuwarsu da korona. Mutum biyu kuma a Gombe, sai wani mutum
ɗaya a Bauchi.