Dakarun Operation Safe Haven da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Nigeria
1 min read
Dakarun Operation Safe Haven da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jihohin Filato da Bauchi da kuma kudancin Kaduna sun samu nasarar cafke mutane 8 da ake zargi da hannu cikin kashe-kashen da ke wakana a kudancin Kaduna.
Kwamandan dakarun Kanal David Nwankonobi ne ya sanar da hakan yauu yayin zantawa da ‘yan jarida a shelkwatar rundunar da ke Kafanchan a Jihar Kaduna.
Kanal Nwankonobi ya bayyana cewa sun samu makamai da dama a hannun ‘yan bindigar da suka kama tare da gawar wani daga cikinsu da ya kasance cikin daya daga cikin wadanda suka kai harin Kudancin Kaduna na baya-bayan nan.
‘Yan bindiga 6 aka kama a karamar hukumar Lere yayin da aka kamu guda biyu a kauyen Chawai da ke tsakainin iyakar Kauru da Zang a karamar hukumar Zangon Kataf.
Wadanda aka kama din sun hadar da Abubakar Ali da Ali Amadu da Bawa Idi da Umar Dikko, sauran sun hadar da Garba Damina da Muhammad Ibrahim Adamu Joseph da kuma William Barnabas.
Kwamandan ya kuma nemi hadin jama’a wajen bayar da bayanai da za su taimaka wajen kama batgarin.