September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnonin Arewa Sun Yi Kiran A Soke Kwangilolin Titunan Da Ba’a Karasa Ba

2 min read

Gwamnonin shiyar Arewa maso
gabashin Najeriya sunyi kira ga gwamnatin tarayyar
kasar, da ta kwace aikin daga ‘yan kwangilar da suka
kasa ci gaba da ayyukansu, domin baiwa wadanda za
su iya aikin cikin takaitaccen lokaci don ci gaban
al’ummar yankin.
Kungiyar gwamnonin sun yi wannan kiran ne a wani
taron gwamnonin shiyar arewa maso gabas da suka
gudanar a garin Maiguduri na kwana biyu. Taron ya
sami halartar Gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi,
Borno, Gombe, Taraba da Yobe.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ne ya
jagoranci taron, ya kuma karanta wa manema labari
jawabin kungiyar Gwamnonin inda ya ce, sun yaba wa
gwamnatin tarayya tare da rundunar sojin kasar a bisa
yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.
To sai dai sun yi kira ga sojojin da su kara kaimi wajen
tabbatar da tsaro a yankunan da suke fama da tashe-
tashen hankula.
Kungiyar Gwamnonin ta kuma yi kira ga Ma’aikatar
Albarkatun Ruwa ta Tarayya da ta tabbatar da an mai
da hankali sosai wajen jan ruwan yankin tafkin Chadi
wanda al’umma da yawa ke amfani dashi.
Sannan sun bukaci da a samar wa ‘yan sanda makamai
na zamani domin taimakawa sojoji wajen yaki da
kungiyar Boko Haram.
Gwamnonin sun yi alkawarin yin aiki tare domin ci
gaban al’ummar su musamman wajen gano ma’adanan
karkashin kasa, kamar su Man Fetur, iskar Gas,
harkokin noma da masana’antu.
Sannan sunyi alkwarin hada kai da gwamnatin tarayya
wajen habbaka makarantun tsangaya da karfafa
karatun Islamiyya da na zamani da kuma hana yawon
barace-barace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *