April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kamen mabarata a Kaduna ya janyo ce-ce ku-ce

2 min read

Rashin jituwa ta kaure tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da
kungiyoyin masu bukata ta musamman saboda fara kamen
mabarata.
Cikin mutanen da aka kama sun hadar da makafi, da guragu, da
kurame mata da tsofaffi.
Wasu daga cikinsu sun shaida wa BBC cewa jami’an tsaro sun cafke
su ne ranar Juma’a, a babban birnin jihar, lokacin da suke bara a kan
tituna.
”An kama mutane da yawa, wasu a Kawo, wasu a Unguwar Sarki,
wasu a Kano Road” In ji wani mabaraci da muka zanta da shi.
Wasu daga cikinsu sun yi korafi a kan munin yanayin wurin da aka
ajiye su, ga shi babu abinci babu ruwan sha kamar yadda mutumin
wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana.
”Wani wuri ne ma, akwai kashin awaki, nan muke fitsari, ga sauro, ba
abinci, kuma tun da aka kama mu babu wanda ya kawo mana abinci,
sai dai wadanda suke da kudi in masu abinci sun kawo su saya”
To sai dai gwamnatin jihar a ta bakin Hafsat Muhammad Baba,
kwamishiniyar kula da walwalar jama’a ta ce daukar wannan mataki
ya zama dole ganin yadda mabaratan ke saba dokokin da aka
gindaya, da kuma rashin bin ka’idojin gwamnati.
Ta kuma ce wasu al’umomin da ke zaune a wuraren da suke bara ne
suka gabatar da ƙorafi a kan yadda almajiran suke ɓata muhalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *