Matsalar fyade: Kauyukan Abuja da ‘yan mata ba sa zuwa makaranta saboda tsoron fyade
2 min read
Burin Hadiza mai shekara 20 shi ne ta zama ‘yar jarida mai karanta
labarai, sai da ta kasa cimma wannan buri saboda fyaɗen da wasu
zauna-gari-banza suka yi mata a hanyarta ta zuwa makaranta.
Hadiza na da shekara 18 aka yi mata fyaɗe, lokacin tana shirin
rubuta jarrabawarta ta ƙarshe a sakandare.
“Ina tare da kawayena muna hanyar zuwa makaranta sai suka auko
mana, sai kawayena suka gudu suka bar ni, har suka zo suka kama
ni suka yi mani fyaɗe.
“Na yi ihu sosai amma babu wanda ya kawo mini ɗauki saboda ba a
cika bin hanyar ba,” in ji ta. Hadiza (ba shi ne sunanta na gaskiya ba). tana zaune ne a ƙauyen
Zhiko da ke Bwari a Abuja babban birnin Najeriya.
Zhiko ƙauyen ƙayau ne wanda babu wasu ababen more rayuwa na a
zo a gani, kuma babu makarantar sakandire kwata-kwata.
Hadiza na tafiyar kilomita da dama kafin ta je makarantarsu da ke
Bwari wadda ake kira New Bwari Secondary School. Daga makarantar zuwa ƙauyensu Hadiza, tafiyar kusan kilomita 10
ne, tana shafe sa’o’i huɗu a tafiyarta da kuma dawowarta makaranta.
Ba ta farin ciki idan tana wannan doguwar tafiyar, kuma tana tafiya
makaranta ne tun 5:00 na asuba.
Domin ganin cewa ta je makaranta kan lokaci kuma ta kauce wa
ramukan kan hanya da kuma tsallake rafi, tana bin wata ƙaramar
hanya da ta ratsa cikin gonaki, kuma ba tsaro a wurin.