June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ridda a Kano: An yanke wa mawaƙi hukuncin kisa bisa yin ɓatanci ga Annabi

1 min read

Wata babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai
shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman ɓatanci
ga Annabi Muhammad S.A.W. tare da wani da ya yi ɓatanci ga
Allah.
Baba Jibo Ibrahim, Kakakin Babbar Kotun Kano, shi ne ya tabbatar
wa BBC da hakan, inda ya ce dukkaninsu suna da damar ɗaukaka
ƙara.
“An yanke wa matashin mai suna Yahaya Aminu Sharif hukuncin
kisa ne sakamakon danganta Annabi S.A.W. da ya yi da shirka,” in ji
Jibo Ibrahim.
“A halin yanzu za a rataye shi har sai ya mutu, kamar yadda sashe na
382 (b) na kundin shari’ar Jihar Kano ta shekara ta 2000 ta tanada. Tun a watan Maris na 2020 ne Aminu Sharif, mazaunin unguwar
Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda aka zarge
shi da yin ɓatancin a cikinta.
Kazalika kotun ta yanke wa wani matashin mai suna Umar Farouq
hukuncin shekara 10 a gidan yari tare da horo mai tsanani bisa laifin
ɓatanci ga Allah Maɗaukakin Sarki.
Alƙali ya yanke wa Umar Farouq hukuncin ne sakamakon shekarunsa
ba su kai 18 kamar yadda kundin manyan laifuka ya tanada.
Ya yi ɓatancin ne yayin da suke yin ce-ku-ce da wani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *