June 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sanatoci goma da basu taba kai kudiri a majalisa ba

1 min read

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da Sanata Adamu Bulkachuwa da tsohon Gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau na cikin Sanatoci goma da suka gaza kai ko da kuduri guda a cikin shekara daya.
Kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa ‘yan majalisu da Sanatoci damar gudanar da dokoki da kudurori, da za su taimaki al’ummar da suke wakilta don ci gaban kasa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito majalisa ta tara da ta fara aiki a 11 ga watan Yuni shekarar da ta gabata, an gabatar da kudurori fiye da 450.
Sai dai rahotanni na nuni da cewa, Sanatoci da dama ne basu shigar da wani kudurin doka ba, baya ga wadancen goma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *