September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban Faransa ya yi tur da kashe ma’aikatan agaji 8 a Ni

2 min read

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi tur da harin da aka kai
wa ma’aikatan jin ƙai a Nijar, inda ya bayyana lamarin a matsayin na
matsorata.
Ya kuma ce zai yi duk abin da zai iya yi don yin ƙarin haske kan
wannan hari da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas, shida
Faransawa da kuma biyu ‘yan Nijar.
Shugaban na Faransa wanda ya zanta da takwaransa Mahamadou
Issoufou na Nijar ya ƙara da cewa ya duƙufa wajen taimakawa don
murƙushe “ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel”.
Hukumomi sun ce wasu mahara ne a kan babura suka far wa
mutanen takwas ciki har da ma’aikatan ƙungiiyar agaji a wani yankin
da ke da ragowar raƙuman dawa cikin Afirka ta Yamma.
Sun dai ce sun tura ɗumbin jami’an tsaro don bin sawun maharan da
suka bi duhun daji suka tsere bayan hallaka mutanen da ƙone Ƙungiyar agajin Faransa ta ACTED ta ce akwai ma’aikatanta da dama
cikin waɗanda aka kashe yayin wata fita don yawon buɗe idanu.
An yi imani shi ne hari irinsa na farko da aka kai wa Turawa ‘yan
ƙasashen Yamma a yankin, wanda fitaccen wuri ne a tsohuwar ƙasar
da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
Gwamnan Tillaberi, Tidjani Ibrahim Kachalla ya ce suna tunkarar
lamarin, kuma za su fitar da ƙarin haske game da wannan hari,
wanda bai ce ga ƙungiyar da ta kai shi ba.
Wata majiya a kusa da hukumomin kula da muhalli ta Nijar ta ce
harin ya faru ne da misalin 11:30 a wani wuri mai nisan kilomita
shida gabas da garin Koure, wanda ba shi da nisa daga Niamey.
Majiyar ta fada wa AFP cewa an harbe akasarin mutanen da harin ya
ritsa da su ne…. Tana cewa sun ga jigidar harsasan da ta ƙare an
yasar da ita a wurin.
A birnin, wani mai magana da yawun dakarun sojin Faransa ya ce
rundunar tsaro ta Barkhane da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a
yankin Sahel, na ba da goyon baya ga dakarun sojan Nijar.
AFP ya rawaito mutanen yankin na tabbatar masa cewa sun ga
jiragen yaƙin Faransa na shawagi ta sama da yammacin ranar Lahadi
yayin da sojojin Nijar suke bincika daji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *