June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu kungiyo sun bukaci al’umma da ringa bawa Jami’an tsaro hadin kai.

1 min read

Hadakar kungiyoyi masu zaman kansu a kudancin Kaduna sun kalubalanci jama’ar dake zaune a yankunan da rikici ya fi shafa da su rinka baiwa jami’an tsaro bayanan da suka kamata.
Hadakar kungiyoyin sun ce jami’an tsaro basa samun bayanan da za su dogara da su wajen gabatar da ayyukan su.
Shugaban hadakar kungiyoyin Dr. Dauda Fadia ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja.
Ya ce shakka babu rashin zuwan jami’an tsaro akan lokaci yayin wasu hare-hare na da nasaba da rashin basu bayanai akan lokaci.
Ta cikin sanarwar kuma Dr. Dauda Fadia ya yabawa jami’an tsaro bisa matakin kama wasu da ake zargi a rikicin kudancin jihar ta Kaduna, inda ya bukaci da ayi gaggawar gurfanar da su gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *