Wata kuniya mai zaman kanta ta rabawa masu bukata ta musamman kudade.
1 min read
Wata kungiya mai zaman kanta dake aiki a jihar Niger ta tallafawa masu bukata ta musamman da tallafin kudi dai-dai lokacin da ake fuskantar matsalolin tattalin arziki.
Shugabar kungiyar Dorothy Nuhu ta bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata, yayin wani taron wayar da kan jama’a masu bukata ta musamman kan annobar COVID-19.
Kungiyar dai ta raba musu kudi da kayayyakin abinci a birnin Minna, a wani mataki na rage musu radadin matsalolin tattalin arziki da aka fuskanta a dalilin COVID-19.
Dorothy Nuhu ta kara da cewa, wanda suka ci gajiyar tallafin sun fara ne daga shekaru 10 zuwa 19 a yankunan Chanchaga da Bosso da kuma Shiroro.
Shugabar na cewa, kowannen su ya samu Naira dubu ashirin da biyar da buhun shinkafa da da dai sauran kayan masarufi.