April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Bindiga Sun Kashe Ma’aikata jinkai

3 min read

Tun farko jami’ai sun bayyyana
faransawan a matsayin ‘yan yawon bude ido, kafin
daga baya, ministan tsaro na Jamhuriyar Nijar Lamarin
ya faru ne a tsakanin karfe 11 zuwa 12 na ranar lahadi
9 ga watan Agusta a kewayen kauyen Koure na yankin
Tilabery dake matsayin wani gandun daji mai jan
hankulan masu yawon bude ido daga sassan duniya
saboda garken rakuman dajin da ke rayuwa a wannan
wuri shekaru aru aru.
Rahotanni na nuni da cewa, faransawa 6 da ‘yan Nijer 2
ne suka gamu da ajalinsu lokacin da wasu mutane akan
babura suka bude masu wuta suka kuma kona motar da
‘yan yawaon bude idon da jagororin su suke ciki, da aka
bayyana cewa motar mallakar kungiyar da ake kira
ONG ACTEL ce.
‘Yan bindiga sun hallaka faransawa 6 a gabashin
Niamey
A cikin hirarsu da Sashen Hausa, gwamnan yankin
Tilabery Tidjani Ibrahim Katchalla ya tabbatar da
faruwar wannan lamari.
Hukumomin sun bayyana cewa nan da nan aka baza
jami’an tsaro domin cafko wadannan mahara sai dai
kuma wasu mazauna birnin Yamai na matukar
mamakin yadda harin ya wakana a yankin da ake
ganin ya fi ko’ ina tsaro a Jamhuriyar Nijar.
Ganin yanayin da aka shiga a yankin Tilbery ya sa
ma’aikatar ministan cikin gidan Jahuriyar Nijar a
shekarar 2019 ta gargadi kungiyoyi masu zaman kansu
su kiyayi zagaya wannan yanki mai makwaftaka da
kasahen Mali da Burkina Faso ba tare da rakiyar
jami’an tsaro ba, saboda haka ake ganin rashin
mutunta wannan tsari ya yi tasiri wajen baiwa ‘yan
bindiga damar kai wannan hari na jiya lahadi.
gawar daya daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka
hallaka a gabashin Niamey,
Wannan na faruwa ne kwana daya kacal bayan da
jami’an tsaro suka murkushe wani harin da ‘yan
bindiga suka shirya kaiwa a karkarar Galmi dake
yankin Tahoua inda rahotanni ke cewa an kashe dan
bindiga daya tare aka kuma cafke wasu daga cikinsu,
yayinda aka bi sawun wasu 2 da suka ranci ta kare.
Saurari rahoton da wakilin muryar Amurka a Yamai
Souley Moumouni Barma ya aiko mana ta sauti.
A cikin hirarsu da Sashen Hausa, gwamnan yankin
Tilabery Tidjani Ibrahim Katchalla ya tabbatar da
faruwar wannan lamari.
Hukumomin sun bayyana cewa nan da nan aka baza
jami’an tsaro domin cafko wadannan mahara sai dai
kuma wasu mazauna birnin Yamai na matukar
mamakin yadda harin ya wakana a yankin da ake
ganin ya fi ko’ ina tsaro a Jamhuriyar Nijar.
Ganin yanayin da aka shiga a yankin Tilbery ya sa
ma’aikatar ministan cikin gidan Jahuriyar Nijar a
shekarar 2019 ta gargadi kungiyoyi masu zaman kansu
su kiyayi zagaya wannan yanki mai makwaftaka da
kasahen Mali da Burkina Faso ba tare da rakiyar
jami’an tsaro ba, saboda haka ake ganin rashin
mutunta wannan tsari ya yi tasiri wajen baiwa ‘yan
bindiga damar kai wannan hari na jiya lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *