July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan bindiga sun kashe Shugaban wata Makaranta.

1 min read

Rundunar ‘yan-sandan Jihar Taraba ta ce, ‘yan bindiga sun kashe shugaban wata makaranta mai zaman kanta Alhaji Danlami Shamaki.
Jami’in hulda da Jama’a na rundunar DSP David Misal ne ya bayyana hakan yayain zantawa da manema labarai.
A cewar sanarwar, an kashe Shamaki ne a yammacin jiya Lahadi akan hanyarsa ta dawowa daga birnin taryya Abuja zuwa jihar Taraba, a karamar hukumar Gassol.
DSP David ya kara da cewa, jim kadan bayan da ‘yan bindigan suka harbi marigayi Danlami Shamaki, suka dauke gawarsa zuwa wani kango inda suka ajiye shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *