June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan Nigeria 288 sun dawo gida daga hadaddiyar daular Larabawa.

1 min read

Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta sanar da cewa ‘yan Najeriya 288 ne suka dawo daga Hadaddiyar Daular Larabawa inda suka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja yau.
Adadin da ya kawo mutane 2,641 kenan da aka kwaso daga Hadaddiyar Daular Larabawa tun bayan barkewar annobar cutar Covid-19.
Hukumar ta wallafa wannan sakon ne a shafinta na tiwita yau, inda ta ce za a yi wa mutanen gwajin kwayar cutar Corona, sannan kuma za a killace su har na tsawon makonni biyu kafin barinsu su tafi garuruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *