June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Ƴan bindiga sun kashe mutane 13 a Benue’

1 min read

Rahotanni daga jihar Benue sun ce ƴan bindiga sun kai hari wani ƙauye
a jihar Benue inda suka kashe mutum 13 a wani rikici mai nasaba da
rikicin masarauta.
Kafofin yaɗa labarai sun ambato rundunar ƴan sandan jihar da ta
tabbatar da harin na cewa an kai harin ne ranar Litinin a ƙauyen Edikwu.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Benue Catherine
Anene ta shaidawa Kamfanin dillacin laraban Faransa AFP cewa
mutane da dama ne suka jikkata a harin yayin da kuma aka kone gidaje
da dama.
Ta ce ƴan bindiga kusan 20 ne suka abka wa ƙauyen suka fara hari kan
mai uwa da wabi.
Kuma a cewarta jami’an ƴan sandan da aka tura sun gano gawawwaki
13 da aka kashe a harin.
Ƴan sandan kuma na zargin rikici kan masarauta ne ya haifar da harin,
kuma ƴan sandan sun ce suna gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *