June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ali Baba ya fara mayarwa malamai kudadensu na Addu’a

1 min read

Hukumar karɓar korafe-korafen rashawa ta Kano ta ce, tuni waɗanda ake zargi da zaftarewa malamai kuɗin addu’a suka fara mayar da kuɗin ga waɗanda suka karɓarwa, ta hannun hukumar bayan da ta kaddamar da bincike a kai.

Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya shaidawa wakilin rediyo DW halin da ake ciki a halin yanzu inda ya ce da llzarge-zargen da aka yiwa mai baiwa gwamnan Kano shawara kan addinai da ɗansa da kuma wasu mutane, na zaftarewa malamai kuɗin addu’ar da gwamna ya basu.
A cewar Muhyi yanzu haka sun mayarwa da mutane bakwai kuɗaɗensu sannan suna ci gaba da faɗaɗa bincike a kai tare da tattara karin hujjoji domin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

Ya kara da cewa, abin da mai baiwa gwamnan shawara da waɗannan mutane suka aikata na wabcewa malaman kuɗin addu’a ya saɓa da doka, kuma a yanzu sun samu gamsassun dalilai waɗanda suka tabbatar da hakan.
Jaridar bustandaily tayi kokarin jin tabakin Ali Baba sai bamu samu jin bakinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *