An kama kishiyoyi da uban yaron da aka ɗaure a turken awaki
2 min readGwamnatin jihar Kebbi ta ba da umarnin gudanar da bincike cikin
gaggawa kan abin da ta kira ‘rashin imanin riƙon sakainar kashin da
aka yi wa yaro’, ɗan kimanin shekara goma mai suna Jibril Aliyu.
Cikin wata sanarwa da Aliyu Bandado Argungu, babban mataimaki
na musamman kan harkar shafukan sada zumunta ga gwamna ya ce
binciken zai yi ƙoƙarin bankaɗo sanadi da kuma gazawar mutanen
da suka kamata su kare rayuwar ƙananan yara da ma manya a jihar.
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana takaici da damuwa kan
yadda Jibril ya shiga garari ba kawai a hannun iyayensa ba, har ma
da gazawar maƙwabtansu da ma ɗaukacin harkokin gudanawar
gwamnati.
Kuma a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na tiwita, gwamnatin
Kebbi ta ce za ta ɗauki nauyin kula da lafiyar yaron da kuma dawo da
shi cikin hayyacinsa.
A cewarta, kishiyoyin babar Jibril ne da mahaifinsa suka ɗaure shi a
turken awaki tsawon shekara biyu a unguwar Badariyya cikin Birnin
Kebbi kafin kuɓutar da shi a ranar Lahadi.
Wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun
nuna yadda jami’an hukumar kare haƙƙin ɗan’adam suka kuɓutar da
Jibril sanye da wata jar riga yana tafiya da ƙyar saboda sirancewa.
Barrista Hamza Attahiru Wala na hukumar kare haƙƙin ɗan’adam ya
ce sun samu Jibril Aliyu ne ɗaure a rumfar awaki, “muka yi magana
da matan (gidan) suka ce eh yaron bai da hankali”.
Ya ce: “Mun same shi yana cin kashi. Kashin busashe (dabbobi)….
had da nashi ɗin, ci yake yi, saboda an ɗaure shi… ga shi nan da
busashe kawai yake hurɗa”.
“An ɗauke shi kawai marah hankali, gaba ɗai hurɗar shi da dabbobi
ne gaba ɗai. Ko magana bai iya ba,” in ji Hamza Wala.
Lauyan ya shaida wa BBC cewa iyayensa sun yi iƙirarin cewa Jibril
Aliyu na da farfaɗiya kuma ba shi da hankali. “Amma mu hay yanzu
ba mu gani ba”.
Sai dai a wani bidiyo an ji ɗaya daga cikin kishiyoyin babar Jibril na
musanta zargin ɗaure yaron. Ta yi rantsuwar cewa wallahi tana ba
shi abinci.
Tuni dai ‘yan sandan jihar Kebbi suka ce sun tsare uban Jibril tare da
matansa uku don ci gaba da bincike kan dalilin da ya sa aka bar shi
cikin mummunan yanayi tsawon lokaci
DSP Nafi’u Abubakar ya ce “Eh to, alhamdulillahi! Yanzu haka yana
asibiti shi yaron…. muna so mu ji sakamakon asibiti me ze nuna ko
rashin abinci ne da tsagwamawa suka sa shi halin da yake ciki”.