July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana Ci Gaba Da Daukar Matakan Kiyaye Tsaro a Jihar Nasarawa

2 min read

Jihar Nasarawa da ke
makwabtaka da jihohin Benue, Kogi da babban birnin
tarayya Abuja na fuskantar matsalolin rashin jituwa
tsakanin kabilu, fadan makiyaya da manoma, farmakin
‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane don neman
kudin fansa.
Gwamna Sule ya ce sun gana da masu ruwa da tsaki
don samar da tsaro a jihar ya kuma ce ranar Laraba 12
ga watan Agusta za a bude wata cibiyar tsaro ta ‘yan
sanda da aka kafa a wani wuri da ake yawan yin fashi
da garkuwa da mutane a kauyen Endehu na Karamar
hukumar Nasarawa Eggon, bayan haka an kuma baza
jami’an tsaro
Mai martaba sarkin Nasarawa, Alhaji Ibrahim Usman
Jibrin ya ce hakkin tsaro na kowa ne kuma a
matsayinsu na iyayen kasa da masu kishin kasa, suna
taimaka wa jami’an tsaro da bayanai don dakile kai
hare-hare.
A bangare guda, sakataren jam’iyyar APC a jihar
Nasarawa Alhaji Aliyu Bello, ya ce yanzu idan aka kama
wani mai babban laifi, zai nemi a kai shi kotu saboda
ya san idan ya je kotu za a bada belinsa. A saboda
haka, ya kamata a sake duba tsarin shari’ar kasar a yi
masa garambawul a kuma samar da kotuna na
musamman da za su iya zartar da hukunci cikin sauri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *