Dalibai 169,144 ne suka yi rajistar jarrabawar NECO zuwa yanzu’
1 min read
Hukumar shirya jarrabawar fita daga sakandare a Najeriya ta National
Examinations Council (NECO) ta fitar da jadawalin jarrabawar ta
shekarar 2020.
Shugaban hukumar, Farfesa Godswill Obioma ne ya bayyana hakan
ranar Talata a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin Jihar
Neja, a cewar rahoton kafar Channels TV.
Shugaban ya ce sun fitar da tsarin yadda ayyukan za su gudana domin
bai nwa makarantun damar shirya wa jarrabawar.
Tsare-tsaren sun haɗa da shirya ɗakunan jarrabawa bisa dacewar
dabarun yaƙi da cutar korona. Daga ciki akwai yin fashi a azuzuwa da
makarantun da kuma ɗabbaƙa yin nesa-nesa da juna a tsakanin
ɗalibai.
game da adadin ɗaliban da za su rubuta jarrabawar kuwa, Farfesa
Obioma ya ce zuwa yanzu 169,144 ne suka yi rajistar jarrabawar
shaidar da ake kira Senior School Certificate Examinatio