April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sama da matasa Miliyan biyar suka nemi shiga shirin Npower

1 min read

Gwamnatin tarayya ta ce sama da mutane miliyan biyar ne suka yi
rajistar shiga cikin shirin samar da aikin yin a wucin gadi na
gwamnatin tarayya wato NPOWER.
Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai
magana da yawun ministar kula da harkokin jinkai takaita abkuwar
ibtila’i da ci gaban jama’a, Halima Oyelade.
Sanarwar ta ce rajistar da aka fara a ranar 26 ga watan shekaran jiya
na Yuni an tsara ne tun farko za a kammala a ranar 26 ga watan jiya
na Yuli amma sakamakon mabukata shiyasa aka kara wa’adin da
mako biyu. Haka zalika sanarwar ta kara da cewa ya zuwa shekaran jiya lahadi
tara ga wannan wata adadin wadanda suka yi rajistar shiga shirin na
NPOWER sun kai miliyan biyar da dubu arba’in da biyu da daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *