Sarkin Kasuwar Sabon Gari ya bukaci Gwamnatin Kano data mai da Filin Wasa na Kano Pillars dake Sabon Gari gurin gudanar da kasuwanci.
1 min read
Sarkin kasuwar ta Sabon Gari Alhaji Nafi’u Indabo ya ce ganin irin muhimmancin da kasuwanci yake da gashi suka ga da cewar filin wasan kwallon kafan na Kano Pillars dake sabon Gari a mai dashi gurin kasuwancin,kuma bawa ‘yan kasuwar da gwamnatin a jihar Kano ta tasa a kasuwar wanda suka zauna a guraren da yake na wucin gadi ne.
Ya kara da cewa sama da ‘yan kasuwa dubu 5000 da gwamnatin ta tasa zasu sami gurin ci gaba da gudanar da kasuwancin nasu matumar aka mai da Filin wasan na sabon Gari gurin kasuwanci.
Alhaji Nafi’u Indabo ya kuma bukaci gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje Kadimul Islam da ya tallafawa ‘yan kasuwar da jari a sakamakon annobar covid 19 wanda da yawa daga cikin yan kasuwar jarin su ya karye.
Ya kuma bukaci Gwamnan da ya saka baki,babban bankin kasa na CBN, ya baiwa ‘yan kasuwar rancen kudi domin farfado da jarinsu.