June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojoji sun kama mutum takwas bisa alaƙa da kashe-kashen Kudancin Kaduna

1 min read

Jami’an tsaro a Jihar Kaduna ta Arewacin Najeriya sun kama mutum
takwas ranar Litinin da ake zargi da hannu a kashe-kashen baya-bayan
nan a kudancin jihar.
Wannan kame ya zo ne bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai, inda
suka kashe mutum aƙalla 30 kuma shi ne mafi girma da rundunar
Operation Safe Haven da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin ta
yi.
Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Kafanchan ranar Litinin,
shugaban rundunar Kanar David Nwankonobi ya ce an yi kamen ne a
unguwanni biyu bayan samun wasu bayanan sirri.
Ya ƙara da cewa an kama mutanen ɗauke da makamai da suka haɗa da
bindgogi ƙirar hannu da gatari masu yawa da kuma babura.
Kanar ɗin ya ce dakarunsa suna ci gaba da samun bayanai kan hari na
ƙarshe da aka kai
Kudancin Kaduna ya fuskanci hare-hare na ‘yan bindiga iri-iri tun daga
watan Yuni, abin da ya jawo asarar rayukan mutane da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *