Wata Kotu a Kano Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Matashi
3 min read
Kotun ta kuma yanke hukuncin
daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali ga wani dan
shekaru 15 saboda samun shi da laifin furta laffuzan da
kotun ta ce sun saba wa shari’ar musulinci.
A cikin watan Maris na wannan shekarar ta 2020 ne
wani matashi mai suna Shariff Yahaya Aminu da ke
unguwar Sharifai a cikin birnin Kano ya wallafa wani
rubutu a shafin Facebook da kuma rera wata waka mai
kunshe da kalaman da shari’ar musulinci ta haramta a
alakanta su da mahallici Allah ta’ala da mazon sa.
Shi kuwa dayan matashin mai suna Umar Faruk Bashir
da iyayen sa ke zaune a unguwar Sharada an tuhume
shi da aikata makamantan wadancan laffuza ne a yayin
da musu ya kaure tsakanin sa da wasu.
Bayan amsa laifukan da ake tuhumar su alkalin babbar
kotun shari’ar Musulincin Kadi Aliyu Muhammad Kani,
ya ce kotu ta yi la’akari da litattafan mazahabar
malikiyya ne wajen yanke hukunci da ya dace da
matasan biyu.
Baba Jibo Ibrahim, da ke zaman kakakin kotunan jihar
Kano ya yi Karin haske akan hukuncin inda ya ce an
yanke wa daya daga cikin matasan hukuncin zaman
gidan gyaran tarbiya na tsawon shekara 10 da kuma
aiki mai tsanani, na biyun kuma da ya danganta
manzon Allah (S.A.W) da shirka, kotun ta yanke masa
hukuncin kisa ta hanyar rataya a karkashin doka mai
lamba 382 ta kotun shari’a. Ko da ya ke, kotun ta basu
dama su daukaka kara nan da kwana 30. Barista Abdul Adamu Fagge tsohon shugaban kungiyar
lauyoyin Najeriya reshen jihar Kano, ya ce kundin
tsarin Mulkin Najeriya ya ba kotun shari’a damar
daukaka kara akan abubuwan da suka shafi rabon
gado, rabon rike yara da sauran abubuwan neman
hakki, amma idan batun laifi ne, dole ne a daukaka
kara a kotun jiha. Ya kuma ce tunda kotun shari’a ce ta
yanke hukuncin, matasan na da dama su daukaka kara
a babbar kotun jiha.
Haka zalika, Barista Abdul Adamu Fagge ya fayyace
wanda doka ta rataya wa alhakin tabbatar da wannan
hukunci bayan kammala shari’a. Ya na mai cewa
gwamnatin jiha ce ke da hakkin aiwatar da hukunci
duk da cewa kotun shari’a ta yanke hukunci.
Shariff Yahaya Aminu, ba shi ne mutum na farko da
kotun shari’ar Musulci ta jihar Kano ta yankewa
hukumcin kisa dangane da aikata irin wannan laifin
ba, tun bayan da jihohi da dama a arewacin Najeriya
suka kafa kotunan shari’ar Musulunci a farkon shekara
ta dubu biyu.
A shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, kotun ta
yankewa wadansu mutane tara da suka hada da mace
guda hukumcin kisa wadanda kotun ta same su da
laifin a karkashi doka ta 404 na kundun tsarin dokokin
shari’ar musulunci ta shekara 2000 ta jihar Kano.
Kotun shari’ar musuluncin ta jihar Kano ta kuma
yankewa wani malamin addinin musulunci mai suna
Abdul-Aziz Dauda da aka fi sani da Abdul inyas,
hukumcin kisa ta hanyar taraya a watan janairun
shekara ta dubu biyu da goma sha shida, bayan ta same
shi da laifin furta kalaman batanci ga manzon Allah.