April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan bindiga sun ce mutum goma

1 min read

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun mutane 10 har da tsohon kansila mai wakiltar mazabar Wanke a birnin Gusau dake jihar Zamfara Salmanu Ahmad.
Sauran sun hada da Aminu Sarki da Lawalli mai chemist da Yusha Jangebe da Malama Nafisa da kuma Alhaji Anas.
Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su Muhammad Bashari Jangebe, ya bayyana wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun shiga kauyen cikin dare inda suka shiga gidajen mutanen da suka yi garkuwa da su.
Bashari ya cemafi-akasarin wadanda aka sace din ‘yan kauwa ne, inda masu garkuwa da mutanen suka bukaci kudin fansa kimanin naira miliyan sittin bayan tattaunawa da su ta wayar tarho.
Tuni dai rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta bakin mai magana da yawunta SP Muhammed Shehu ta ce ta baza jami’anta domin nemo mutanen da aka sace.a a fadin jihar baki-daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *