June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Masu Fyade

1 min read

Kakakin rundunar ‘yan sandan
jihar Taraba DSP David Misal ya bayyana yadda aka
kama wadannan mutanen a wata ganawa da manema
labarai.
DSP Misal ya bayyana cewa, “Ahmadu Garba magidanci
dan kimanin shekaru 65 da haihuwa, na daga cikin
wadanda aka kama bisa zargin lalata da wata karamar
yarinyar ‘yar kimanin shekaru 11 da haihuwa. Bayan
haka sai Abubakar Bala, dan shekara 37 wanda ke
sana’ar wankin mota da kuma Suleiman Ahmadu dan
shekara 28 wanda shima aikin gadi ya ke yi, kuma
yarinyar ta yi zama da shi tsawon wata 3 yana lalata da
ita a cewarsa.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma ja hankalin
iyaye akan su ci gaba da sa ido da kuma maida hankali
kan ‘yayansu saboda yadda zamani ya lalace. A baya Mallama Binta Khalid Adam, wata uwa kuma
yar fafutukar sauya tarbiyar al’umma ta yi karin haske
akan dalilan karuwar ayyukan lalata da kuma fyade ga
kananan yara da ta kasa su gida uku.
Ta ce kashi na farko sune masu harka da miyagun
kwayoyi, na biyu kuma manyan mutane da ke aikata
wannan mummunar dabi’a saboda tsubbu. Sai kashi na
uku, wanda su kuma hali ne, muddin suka ga wata
mace tunaninsu shine su keta haddinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *