Coronavirus a Najeriya: Fiye da mutum 400 sun kau da cutar ran Talata
3 min read
An sake gano mutum 423 da cutar korona a Najeriya, cewar
hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta ƙasar a ranar Talata, yawan
mutanen da annobar ta harba ya kai 47,290.
Bayanan da hukumar NCDC ke fitarwa a kullum, sun kuma nuna
cewa cutar korona korona ta yi sanadin mutuwar mutum shida a
ranar Talata.
Yawan mutanen da hukumomi suka ba da rahoto sun mutu
sakamakon annobar 956 tun bayan ɓullarta Najeriya.
Alƙaluma sun nuna cewa mutum 117 sun harbu da cutar a jihar
Lagos, wurin da annobar ta fara bulla, kuma ta fi ƙamari.
Ko da yake, a baya-bayan nan an yi matuƙar samun raguwar yawan
waɗanda cutar ke shafa a cikin jihar.
Ƙididdigar NCDC ta kuma bayyana cewa marasa lafiya 263 sun
warke kuma an sallame su daga cibiyoyin kwantar da masu korona
na ƙasar ranar Talata. Haka kuma NCDC ta ba da rahoton gano sabbin masu cutar 40 a
Abuja, babban birnin Najeriya. Sai jihar Ondon, inda mutum 35 suka
kamu.
Akwai kuma mutum 28 da gwaji ya tabbatar da kamuwarsu a jihar
River, a Osun, korona ta harbi mutum 24.
Daga Binuwai, akwai mutum 21, jihar Abia, 19 kamar dai alƙaluman
masu cutar da aka gano a Ogun.
Sai jihar Ebonyi, mutum 18. A jihohin Kwara da Delta, an ba da
rahoton kamuwar mutum 17 cikin kowaccensu.
Kaduna ta sake gano masu cutar korona 15, sai mutum 14 a jihar
Anambra. 11 kuma daga jihar Ekiti.
A Kano an gano sabbin masu korona tara, a jihar Imo mutum shida
sai Gombe huɗu.
NCDC ta kuma ba da rahoton samun mutum uku dauke da cutar a
kowacce cikin jihohin Taraba da Oyo.
Bauchi kuma da Nasarawa da Edo, mutum dai-dai aka gano sun
kamu da korona ranar Talata Muhimman bayanai kan annobar korona
Ranar Laraba 16 ga watan Yuni ne Najeriya ta ba da rahoton mutuwar
mutum 31 sakamakon cutar ta korona, shi ne adadi mafi yawa na
mace-macen da aka samu cikin sa’a 24 a ƙasar.
Sai kuma Laraba 1 ga watan Yuli, inda aka samu adadi mafi yawa
zuwa yanzu na mutum 790 da suka kamu da cutar.
An fara gano ƙwayar cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen
kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin
jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris
a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an
sallame su daga asibiti.
A ranar Juma’a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin
mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban
Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin
korona a kasar.
Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da ke kudu maso kudancin
Najeriya shi ne wani jagoran al’ummar jiha na baya-bayan nan da ya
kamu da cutar korona ranar Laraba 1 ga watan Yuli.
Tun da farko gwamnoni irinsu Nasir El-Rufai na Kaduna da Bala
Mohammed na Bauchi da Seyi Makinde na Oyo da Okezie Ikpeazu na
Abia, da Rotimi Akeredolu na jihar Ondo duk sun kamu da annobar.
Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya yawan gwaje-gwajen da
suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji fiye da dubu ɗaya
cikin sa’a 24.