July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kano Pillars ta aika sakon alhini ga dan wasa Christopher Madaki

1 min read

Hukumar gudanarwa ta kungiyar kwallan kafa ta
Kano Pillars, karkashin jagoran cin Alhaji Surajo Shuaibu Yahaya, ta
mika sakon ta’aziyya ga dan wasan bayan tawagar kungiyar
Christopher Madaki, bisa rashin Mahaifiyarsa da yayi.
Christopher Madaki Maichibi, yayi rashin Mahaifiyarsa a jiya Litinin
a garin Jos, bayan bayyana rasuwar ta. Alhaji Surajo Shuaibu
Yahaya, ya ce kungiyar da ‘yan wasanta sun kadu matuka da jin
labarin , kana suna cikin alhini tare da jimami ga dan wasan
kasancewar wannan mawuyacin hali da ya shiga na rashin.
Shugaban ya shirya tawaga karkashin jagorancin Jami’in hulda da
Jama’a na Kano Pillars, Rilwanu Idris Malikawa Garu (Dagacin
Malikawa) gami da wasu daga cikin ‘yan wasan domin wakilcin
kungiyar wajen yiwa dan wasa Christopher Madaki ta’azziyya.
Shu’aibu Yahaya ya bayyana rashin mahaifiyar da Madaki yayi a
matsayin rashi babba ga daukacin ‘yan wasan kungiyar baki daya,
ya kuma roke su da suyi hakuri da hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *