March 5, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Masu zanga-zanga sun sake komawa kan tituna

2 min read

An sake yin wata zanga-zangar adawa da gwamnati a Bamako
babban birnin kasar Mali.
Dubunnan mutane ne suka yi zanga-zangar suna kira ga Shugaba
Ibrahim Boubakar Keita, da ya sauka daga karagar mulki.
Suna nuna fushi ne da yadda hare-haren masu ikirarin jihadi ke ci
gaba karuwa, baya ga matsalar cin hanci da rashawa da suke zargin
ta addabi kasar.
Shugaban masu zanga-zangar, dan ra’ayin mazan jiya Mahmud
Dicko, ya fada wa taron cewa za su yi nasarar dawo da martabar
kasar.
Ya ce zai sake yin kokarin tursasawa shugaban ya sauka.
Yunkurin sulhu da shugabannin yankin Afrika suka yi bai kai ga gaci
ba, bayan da masu zanga-zangar suka yi shuri da kiran kafa
gwamnatin gamin gambiza Me ya sa mutane ke zanga-zanga?
Wannan zanga-zanga ita ce ta uku tun cikin watan Yuni.
Zanga-zanga ta fara ne bayan ƙawancen ‘yan adawa sun yi watsi da
sassaucin da Shugaba Keita ya ɓullo da shi don kawo ƙarshen rikita-
rikitar siyasa kan dambarwar zaɓen ‘yan majalisar dokoki a watan
Maris.
A makon nan ‘yan adawa sun ce tafiyarsu ta jingine buƙatarta ta
neman Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya sauka. Sai dai har yanzu
ta buƙaci gudanar da zanga-zanga saboda tana neman ƙarin sauye-
sauye.
Keita ya hau mulki wa’adi na biyu tsawon shekara biyar ne a 2018 sai
dai yana fuskantar ƙarin adawa game da bazuwar tarzomar masu
iƙirarin jihadi da kuma matsalar tattalin arziƙi.
Al’ummar Mali dai na fatan cewa masu iƙirarin jihadi, waɗanda su ne
da hannu wajen ƙaruwar rikici a yankin arewa da tsakiyar ƙasar, ba
za su yi amfani da wannan turka-turka da ta taso ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *