July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan sanda sun cafke wani tsoho mai bada hayar kananan Yara Mata.

2 min read

Rundunar ‘yan sandan Najeriya shiyyar jihar Taraba ta ce tana
gudanar da bincike kan wani tsoho mai shekara sittin da bakwai da
kuma ƙarin mutum biyu, bisa zargin killace wata yarinya ‘yar
shekara goma sha ɗaya, suka yi mata fyaɗe.
Ana zargin mutanen uku da a halin yanzu rundunar ‘yan sandan jihar
ta ce tana tsare da su, da yin lalata da yarinya tsawon lokaci ta
hanyar karɓa-karɓa a Jalingo, babban birnin jihar.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Taraba ya ce tsohon ya riƙa
karɓar kuɗi daga wani mutum da kan je a mota ya ɗauki yarinyar ya
tafi da ita don aikata lalata.
“Sannan har yanzu akwai wani wanda da alama shi wannan dattijon
yana ba da hayanta a wajenshi, wanda kullum da moto yake zuwa ya
ɗauke ta, ya kai ta wani wuri, ya je yai lalata da ita,” cewar DSP David
Misal.
Ya ce shi ma mai motar tuni suka fara bin sawunsa don kamo shi. Ɗan sandan ya ce tsohon ne ya fara tsintar wannan ƙaramar yarinya
a tashar motar birnin Jalingo, kuma ya ajiye ta a hannunsa tsawon
wata uku.
“Yana aikin gadi a wani gidan mai, sai ya shigar da ita, ya yi ta lalata
da ita zuwa kusan wata uku da suka gabata. Abin mamaki kuma ba
shi kaɗai ya tsaya ba.
David Misal ya ce tsohon ya kuma gayyato abokansa biyu waɗanda
suka riƙa zuwa suna yi mata fyaɗe kafin asiri ya tonu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *