Yaran da ba sa zuwa makaranta a Zamfara sun zarce miliyan daya
2 min read
Gwamnatin jihar Zamfara a Najeriya ta ce kimanin yara miliyan daya
ne ba sa zuwa makaranta a jihar, abin da ke kara fito da matsalar da
bangaren ilimi ke ciki karara a fili.
Sai dai a wani mataki na rage matsalar a yanzu, ta ce ta bullo da
wani shiri na gwama karatun boko da na allo, da kuma ciyar da
almajirai a makarantun allonsu.
Abubakar Aliyu Maradun, shi ne shugaban hukumar ilimin bai daya ta
jihar Zamfara, ya kuma shaidawa BBC cewa shirin ya samo asali ne
daga wata kidaya da aka yi, da ta nuna cewa a Najeriya akwai yara
miliyan goma da basa zuwa makaranta, kuma miliyan daya daga
cikinsu Zamfarawa ne.
”Babbar manufar ita ce bawa wadannan yara damar lakantar ilimin
dukkanin bangarorin biyu, da kuma dakile matsalar barace-barace” in
ji shi. Ya ce za a fara shirin ne da makarantun allo 280 a kananan
hukumomi 8, kuma da yara dubu talatin za a fara.
”An tanadi kayayyakin karatu, littattafan yara da kuma malaman,
sannan muna basu abinci sau daya a kullum”
Jihar Zamfara dai na fama da matsalar tsaro a halin da ake ciki,
sakamakon hare-haren yan fashin daji. Ana danganta rashin tsaro a jihar a matsayin daya daga cikin
mantsalolin da ke kawowa bangarori da dama tawaya, ciki har da na
ilimi.
Gwamnatin jihar ta sha cewa tana iya bakin kokarinta domin kawo
karshen matsalar, ta yadda jama’a za su samu damar ci gaba da
rayuwa cikin nutsuwa da aminci.