September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Karancin wuraren binne mutane ya tayar da hankalin jama’ar Kano

2 min read

Masu kula da maƙabartu a jihar Kano da ke Najeriya sun koka bisa
yadda ake fama da ƙarancin wuraren binne mamata a maƙabartun
da ke jihar.
Masu aiki a makabartu irin na Abbatuwa, da Gidan Gona sun shaida
wa BBC cewa wuraren binne mamata sun yi matuƙar ƙaranci ta
yadda a wasu lokutan sai dai su hada gawarwaki biyu a kabari guda
saboda cikar da makabartun suka yi.
Wakilin BBC na Kano Khalifa Shehu Dokaji wanda ya halarci wasu
makabartu, ya gane wa idanunsa yadda suka yi cikar kwari.
Ya ce wasu daga cikin hanyoyin da ake bi a cikin makabartun na kara
tsukewa sannan akwai kaburbura wasu a manne da juna, inda filin
da ke tsakaninsu ba shi da yawa, kuma wasun su babu inda mota za
ta bi ta shiga cikin makabarta.
Malam Danbaba Muhammad, shugaban ma’aikatan makabartar
Abbatuwa, ya ce akwai bukatar gwamnatin jihar ta samar da sabbin
makabartu a unguwannin da ke Kano, saboda yanzu a tsakanin
kaburbura kadai suke iya binne gawa sakamakon yadda ta cika. Hakika muna da matsaloli a makabartunmu; wani lokacin idan mun
zo binne mutane muka ga wani(gawa) wanda lafiyar kalau babu abin
da ya same shi, sai mu yi kasa da shi mu dora wani a kansa. Wani
lokacin kasusuwa za mu tarar, sai mu baje mu sa wani a kai,” in ji
shi.
Ya kara da cewa rashin isasshen wurin binne mutanen abin tayar da
hankali ne musamman idan aka yi la’akari cewa har yanzu gwamnati
ba ta samar da mafita game da matsalar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *