June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yanzu haka ana gudanar zanga-zanga

1 min read

Ƴan sanda a Ivory Coast sun tarwatsa magoya bayan ƴan dawa da ke
zanga-zangar adawa da ƙudirin shugaba Alassane Ouattara na neman
wa’adi na uku akan mulki.
Masu zanga-zangar sun bijerewa haramcin zanga-zangar, inda suka
dinga ƙone tayoyi a Abidjan babban birnin ƙasar.
Akalla mutum biyu aka bayar da rahotannin an kashe a zanga-zangar a
ranar Laraba a rangama tsakanin magoya bayan jam’iyyun ƴan adawa
kuma magoya bayan jam’iyya mai mulki.
Mista Ouattara ya yanke shawarar neman wa’adi na uku bayan
jam’iyyarsa ta amince masa. A makon da ya gabata Firaminista
Amadou Gon Coulibaly ya rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *