Ƴan bindiga sun kashe ɗan majalisa a Bauchi kuma suka sace matansa
1 min readWasu ƴan bindiga da ba a tantance ba sun kashe wani ɗan majalisar
jihar Bauchi mai wakiltar mazaɓar Dass.
Rahotanni sun ce ƴan bindiga sun shiga gidan Honarabul Musa Kante
da dare ranar Alhamis suka kashe shi. Yana cikin ƴan majalisar da aka
bayyana sun kamu da cutar korona a kwanakin baya kafin ya warke
daga cutar.
Ana tunanin ƴan fashi ne suka kashe ɗan majalisar inda kuma
rahotanni suka ce sun yi awon gaba da matansa biyu bayan sun kashe
shi.
BBC ta fahimci cewa yau za a yi jana’izarsa da misalin karfe tara da
rabi na safe.