June 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An buɗe kasuwar Sheikh Abubakar Gumi bayan wata hudu a rufe

1 min read

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta buɗe babbar kasuwar jihar mai suna Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, bayan shafe fiye da watanni hudu kasuwannin jihar suna rufe. Gwamnan jihar Kadunan Malam Nasir El-Rufai dai ya ce an dauki matakin rufe daukacin kasuwannin jihar ne don hana yaduwar cutar Korona. BBC ta ziyarci kasuwar da aka fi sani da Central Market da ke kwaryar birnin Kaduna, wanda shi ne babban birnin jihar. Kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ta kasance kasuwa mafi girma a fadin jihar da dubban jama’a daga ciki da wajen jihar ke kwararowa domin yin hada-hada. Gwamnatin jihar ta ce ta yanke shawarar bude kasuwar bayan data gamsu da matakan kariyar hana yaduwar cutar Korona wanda aka dauka tsakanin gwamnatin da shugabannin ‘yan kasuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *