July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An gurfanar da mahaifin yaron da aka ɗaure a turken dabbobi

1 min read

Rundunar ƴan sanda a jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya ta bayyana
cewa ta gurfanar da mahaifin yaron nan da aka ɗaure a turken dabbobi
a gaban kuliya, bayan ta kammala bincike da ta ke yi a kan lamarin.
Rundunar na tuhumarsa ne da tauye haƙƙin yaron, sakamakon gazawar
mahaifin wajen sauke wajibinsa na kula da ɗan da ya haifa.
A karshen makon jiya ne jami`an wata ƙungiyar farar hula suka
bankaɗo inda aka ɗaure yaron, wanda daga nan ƴan sanda da
gwamnatin jihar Kebbi suka shiga cikin maganar.
DSP Nafi`u Abubakar kakakin rundunar ƴan sanda, ya shaida wa BBC
cewa mahaifin ya tabbatar masu da cewa an haifi yaron ne da wata
rashin lafiyar taɓin hankali saboda ya gaji da neman magani ne ya
ɗaure shi don ya hana shi fita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *