An kama mahaifin da ya tsare ɗansa tsawon shekara uku a Kano
1 min read
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce an samu nasarar ceto wani
matashi da aka tsare shi a cikin gidansu tsawon shekara uku ba tare
da ba shi damar fita ba.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Haruna Kiyawa, ya tabbatar
wa BBC hakan ne a ranar Juma’a da safe.
A ranar Alhamis da yamma ne bidiyon da ke nuna yadda aka kuɓutar
da yaron ya watsu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta da
muhawara a faɗin ƙasar.
A cikin bidiyon an ga yadda wasu mutane suka ɗauke shi suka saka
shi a cikin motar ‘yan sanda aka tafi da shi, yayin da wasu mutanen
ke tattauna wa da shi yana nuna alamun farin ciki.
Sannan ƙasusuwan jikinsa duk sun fito, abin da ke nuna alamun
yunwa da rashin lafiya.
Wannan lamari na zuwa ne a ranar da ‘yan sanda suka gurfanar da
mahaifin yaron da aka ceto a Birnin Kebbi ranar Lahadi, wanda aka
zargi matan ubansa da ɗaure shi a turken dabbobi tsawon shekara
biyu.
Mahaifin Ahmed ya shaida wa ‘yan sanda cewa dalilinsa na ɗaukar
wannan mataki shi ne yana zargin ɗansa da mu’amula da miyagun
ƙwayoyi. R