June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An samu karuwar yawan marasa ayyukan yi a Najeriya

1 min read

Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce adadin rashin aikin ya kai kashe
27.1 a alƙalumman farko da ta fitar tun 2018.
Adadin ya ƙaru ne daga 23.1 na rashin aikin yi da aka fitar a 2018 zuwa
27.1 a 2020.
Hukumar ta ce sama da kashi ɗaya bisa huɗuna ma’aikata sun rasa
ayyukan yi a 2020. Kuma yawan adadin matasa da suka rasa ayyukan yi
tsakanin ƴan shekara 15 zuwa 34 ya kai kashi 34.1 wanda shi ne adadi
mafi girma.
Annobar korona ta kara haifar da taɓarbarewar tattalin arziki a Najeriya
bayan faduwar farashin danyen mai da cutar ta haifar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *