Ana ci gaba da samun Ambaliyya a wasu kananan hukumomin Jihar Kano
1 min read
Wani binciken masana ya nuna cewa akwai kananan hukumomi 25 a jihar Kano dake cikin hadarin fadawa Ambaliyya ruwa a damunar bana.
Rahoton ya ce matukar gwamnati bata fargaba,a kalla mutane sama da miliyan daya, ka iya rasa gidajensu.
A baya-bayannan dai an sami ambaliyya a karamar hukumar Bagwai a Kano wacce daya ce daga cikin jihoyin dake fama da matsalar ambaliyyar ruwan.